Mutane sama da 50 ne suka mutu a wani harin Bam a Sri Lanka
Wallafawa ranar:
Wasu bama-bamai da suka tashi a wasu gidajen kwana guda uku da aka sani da Otels da wasu mujami’un kasar Sri Lanka sun haddasa mutuwar mutane da dama a birnin Colombo na kasar Sri Lanka.
Wadanan hare-hare sun wakana ne a lokacin da kiristoci a Sri Lanka ke gudanar da addu’oIn su’, dangane da yi tuni da ranar da suka yi amannan an bayar da Isa Almasihu domin a giciyeshi.
Akalla mutane 52 ne yanzu haka aka tattance sun rasa rayukan su, sama da 160 ne aka garzaya da su asibiti inda ake ci gaba da kawo wasu yanzu haka .
Lamarin ya wakana daf da gidan Firaministan kasar .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu