Adadin wadanda suka mutu a harin Sri Lanka ya tasamma 300
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga kasar Sri Lanka na nuni da cewa adadin wadanda harin, bama-bamai a majami'u da Otel ya hallaka ya kai 290 baya ga wasu fiye da 500 da suka samu munanan raunuka.
Bayanan baya-bayan nan da gwamnatin Sri Lanka ta fitar ya nuna cewa an samu rasuwar wasu daga cikin wadanda suka jikkata a harin wanda har bama-bamai 8 suka tashi ciki har da 2 na kunar bakin wake.
Yayin faruwar lamarin dai mutane 207 aka tabbatar da mutuwarsu a wasu majami'un kasar da Otel, dai dai lokacin da ake tsaka da shagulgulan Easter.
Tuni dai gwamnatin kasar ta bakin Firaminista Ranil Wickremesinghe ta sanar da kama wasu mutanen 8 da ake zargi da hannu wajen kai jerin hare haren.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu