Sri Lanka

Sri Lanka ta gano maharan da suka kashe mutane 290

Daya daga cikin Majami'un da aka kai wa hari a Sri Lanka
Daya daga cikin Majami'un da aka kai wa hari a Sri Lanka Reuters/路透社

Gwamnatin Sri Lanka ta bayyana wata karamar kungiyar masu tsattsauriyar akidar Islama a matsayin wadda ta kai harin bama-baman da ya kashe kusan mutane 300 a karshen mako.

Talla

Mai magana da yawun gwamnatin kasar, Rajitha Senaratne ya ce, a halin yanzu ana gudanar da bincike don sanin ko Kungiyar National Thowheeth Jama’ath ta samu goyon baya daga ketare wajen kai farmakin kan Majami’u da Otel Otel a yayin bukin Easter a kasar.

Babu wata cikakkiyar masaniya game da wannan karamar kungiya, amma wasu takardun bayanai da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya samu kwafinsu, sun nuna cewa, a ranar 11 ga wannan wata na Afrilu, shugaban rundunar ‘yan sandan kasar ya yi gargadi, in da yake cewa, bayanan sirrin da suka samu daga ketare sun ce, wannan kungiya na shirin kai hare-hare kan Majami’u da kuma Ofishin Jakadancin India.

A can baya dai, kungiyar ta yi kaurin suna wajen lalata gumakan mabiya addinin Buddha a kasar.

Tuni dai aka cafke mutane 24 da ake zargi da hannu a kazamin farmakin, amma kawo yanzu ba a fitar da cikakkun bayanai akan mutanen ba.

Fadar shugaban kasar ta Sri Lanka ta ce, an kafa dokar ta-baci ne domin jami’an tsaro su tabbatar da tsaron lafiyar jama’a, yayinda kuma gwamnati ta bukaci taimakon rundunar ‘yan sandan kasa da kasa domin gudanar da bincike kan hare-haren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI