Sri Lanka

Tawagar kwararru za ta bincike harin Sri Lanka

Wasu daga cikin jami'an tsaron Sri Lanka bayan harin ta'addancin da ya kashe kusan mutane 300
Wasu daga cikin jami'an tsaron Sri Lanka bayan harin ta'addancin da ya kashe kusan mutane 300 Jewel SAMAD / AFP

Hukumar ‘Yan Sandan Kasa da Kasa za ta tura tawagar kwararru domin gudanar da bincike kan harin da ya hallaka mutane kusan 300 a Sri Lanka.

Talla

Hukumar ‘Yan Sandan Kasa da Kasa ta ce, za ta tura kwararrun jami’an gudanar da binciken ne bayan gwamnatin Sri Lanka ta bukaci haka.

Kwararrun Jami’an sun hada da gwanayen binciken wuraren da aka kaddamar da farmaki da tashin bama-bamai da tantance wadanda harin ya shafa har ma da yaki da ayyukan ta’addanci.

Sakatare Janar na Hukumar ‘Yan Sandan Kasa da Kasar, Juergen Stock ya ce, za su ci gaba da bai wa Sri Lanka duk wani taimako da take bukata.

Mahukuntan kasar sun yi amanna cewa, Kungiyar National Thowheeth Jama’ath ta masu tsattsauriyar akidar Islama ce ta kaddamar da harin da ya lakume kusan rayuka 300 tare da jikkata fiye da 500 a Majami’u da Otel Otel a kasar.

A bangare guda, Amurka ta lashi takobin ci gaba da yaki da masu tsattsauriyar akidar Islama, in da Sakataren Harkokin Wajenta, Mike Pompeo ke cewa, irin wannan akida na ci gaba da zama babbar barazana.

Fadar Gwamnatin Amurka, White House ta bayyana farmakin na Sri Lanka a matsayin daya daga cikin munanen hare-haren ta’addanci da aka kaddamar tun watan Satumban 2001.

Tuni gwamnatin Sri Lanka ta ayyana dokar ta baci a duk fadin kasar wadda za ta fara aiki daga tsakiyar daren Litinin domin bai wa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI