Isa ga babban shafi
Amurka-Trump

Majalisar dokoki ba ta da hurumin tsige ni- Trump

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump 路透社。
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 1

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, Majalisar Dokokin Kasar bata da hurumin tsige shi, sakamakon rahotan mai bincike Robert Mueller kan yadda ya yi kokarin katsalandan kan binciken.

Talla

A sakon da ya aike ta Twitter, shugaba Trump ya ce, ana amfani da aikata manyan laifuffuka ne wajen tsige shugaban kasa, kuma ta tabbata cewar babu wani laifi ko hadin kai wajen hada baki da zai ba da damar tsige shi.

Trump ya shaida wa Amurka cewar, 'Yan Democrat ne suka aikata laifi amma ba shugaban Republican ba.

Tuni Majalisar wakilai ta bukaci gabatar mata da daukacin rahotan binciken domin yin nazari kan matakin da za ta dauka nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.