Nissan

Faransa da Japan za su karfafa kamfanin Nissan

Firaministan Japan, Shinzo Abe da shugaban Faransa, Emmanuel Macron a birnin Paris
Firaministan Japan, Shinzo Abe da shugaban Faransa, Emmanuel Macron a birnin Paris REUTERS/Philippe Wojazer

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da Firaministan Japan Shinzo Abe, sun yi alkawarin ci gaba da mara wa kawancen da ke tsakanin kamfanonin kera motocin Renault da kuma Nissan, biyo bayan dakatar da Carlos Ghosn daga shugabancin wannan kamfanin saboda zargin rashawa.

Talla

Shugabannin kasashen biyu sun ce, za su ci gaba da aiki tare ne karkashin wani sabon kawance da suka baayyana a matsayin na musamman, wanda zai mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da kuma hulda ta bangaren aikin soji.

Sakamakon zargin almundahana da kudaden kamfanin da ake yi wa Carlos Ghosn wanda asalinsa Bafarenshe ne tun cikin watan Nuwamban da ya gabata, an fara nuna fargaba dangane da makomar kawancen da ke tsakanin kamfanonin biyu.

Firaminista Abe wanda ya kaddamar da ziyara a kasashen Turai da Arewacin Amurka, ya halarci wata liyafar cin abincin rana da shugaba Macron ya shirya masa, in da suka tattauna dangane da batutuwan da suka shafi taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya da zai gudana cikin watan Juni a kasar ta Japan.

To sai dai batun makomar wannan kawance da aka kulla tun 1999 tsakanin manyan kamfanonin kera motocin biyu na duniya wato Renault da Nissan ne ya fi daukar hankulansu a wannan ganawa a cewar fadar Elysees.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI