Erdogan-Macron

Erdogan ya yaba da matakin Macron kan kisan kiyashin Armenia

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Murad Sezer

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan karon farko tun bayan barkewar yakin cacar baka tsakaninsa shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yaba da kokarin Faransar na ware rana guda don tunawa da kisan kiyashin Armenia a shekarar 1915.

Talla

Cikin jawaban Erdogan ya ce Faransa ce babbar kasa guda daya tilo daga yankin nahiyar Turai da ta girmama ranar tun bayan 2001.

A Larabar da ta gabata ne dubban al’ummar Faransa suka gudanar da wani makokin yini guda don alhinin mutanen fiye da miliyan 1 da dubu dari biyu da dakarun sojin daular Ottomon suka yiwa kisan gilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.