Amurka

Shugaba Trump na Amurka ya sharara karya fiye da dubu 10

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Leah Millis

Jaridar Washington Post da ake wallafawa a Amurka ta yi zargin cewar shugaba Donald Trump ya sharara karairayi sama da 10,000 a kwanaki 800 da ya yi a karagar mulki, a daidai lokacin da yake zargin kafofin yada labarai da wallafa labaran karya.

Talla

Wadannan alkaluma da Jaridar Washington Post ta wallafa sun biyo bayan binciken kwakwaf da jaridar ta gudanar tun lokacin da shugaba Donald Trump ya cika kwanaki 100 a karagar mulki.

Jaridar ta ce, a farkon shekarar 2017 shugaban na Amurka na karya ko bada labaran karya 5 a kowacce rana, amma kuma adadin ya karu cikin watanni 7 da suka gabata, inda shugaban kan yada labaran karya 23 a kowacce rana ta kafarsa ta Twitter, ko taron magoya bayansa ko kuma ganawa da manema labarai.

Washington Post ta ce, kashi 22 na karairayin da shugaban ke yi, yana yin su a taron magoya bayansa, inda yake jaddada matsayinsa na sake gina Amurka.

Jaridar ta ce, a ranar Juma’ar da ta gabata, irin kararayin da shugaba Donald Trump ke yi suka zarce 10,000, kwana guda kafin halartar wani taron magoya bayansa a Green Bay dake Wisconsin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI