Trump-Haftar

Zantawar waya tsakanin Trump da Haftar ya janyo cece-kuce

Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da ya ke zantawa ta waya da Khalifa Haftar na Libya
Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da ya ke zantawa ta waya da Khalifa Haftar na Libya Reuters

Kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa Janar Khalifa Haftar mai iko da amfi akasarin yankunan kasar Libya, don yaba masa kan murkushe mayakan ISIS, ya fusata wasu ‘yan majalisar dattijai musamman na jam’iyyar Republican.

Talla

Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican kuma mamba a kwamitin majalisar dattijan Amurka kan harkokin kasashen ketare, ya zargi Donald Trump da goyon bayan bangare daya a kasar ta Libya mai fama da rikici.

A zanatawrsa da manema labarai Sanata Lindsey Graham ya yi bayani da cewa ''Bani da cikakkar masaniya kan kiran Janar Khalifa Haftar da Shugaba Donald Trump ya yi ta wayar tarho, sai dai abinda na ke da yakini akai shi ne akwai wata a kasa''.

Sanatan ya kara da cewa ''Ina kasar Tunisia a lokacin da Trump ya kira Haftar da sunan Janar daga Gabashin Libya, tare da yaba masa kan rawar da ya taka wajen fatattakar mayakan ISIS daga kasar ta Libya''.

Dan Majalisar Dattijan na Amurka ya kuma kara da cewa ''muna da yakinin wannan kiran wayar na tattare da wata manufa, da za ta yi tasiri mai karfi kan yankin, domin za’a yi tunanin Amurka na goyon bayan bangare guda''.

Kawo yanzu dai ana ci gaba da fuskantar rikici a kasar ta Libya wanda shi ne rikici mafi muni da ya barke tun bayan hambarar da gwamnatin Mua'ammar Gaddafi a shekarar 2011.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI