Isa ga babban shafi
AMurka- Iran

Takunkuman Amurka kan Iran sun fara aiki

Masana sun ce, matakin zai yi mummunar illa kan tattalin arzikin wasu kasashe
Masana sun ce, matakin zai yi mummunar illa kan tattalin arzikin wasu kasashe REUTERS/Raheb Homavandi/File Photo/File Photo
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

A yau ne takunkuman Amurka za su fara aiki kan kasashen da ke sayen man fetur daga Iran, matakin da zai kara matsin lamba kan tattalin arzkin kasar. Tuni masa tattalin arziki suka bayyana cewa, wannan matakin zai haifar da tsadar man fetur tare da gaggauta tashin farashin kayayyaki, baya ga yin mummunar illa ga tattalin arzikin India.

Talla

A cikin watan Mayun da ya gabata ne, shugaban Amurka Donald Trump ya janye kasar daga yarjejeniyar nukiliya da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya, yarjejeniyar da ta sassauta takunkuman da aka kakaba wa kasar bayan ta amince ta dakatar da shirinta na nukiliyar.

Sai dai a cikin watan Nuwamba, Amurka ta sake maido da takunkuman fitar da man fetur akan Iran, yayinda ta baiwa wasu kasashe takwas da suka hada da aminanta wa’adin watanni shida da su soke gudanar da harkar sayen mai daga Iran.

A cikin makon jiya ne, Amurkar ta sanar cewa, takardun izinin hada-hadar man fetur din da Iran da wadannan kasashe suka mallaka, za su daina aiki daga yau ranar 2 ga watan Mayu.

Wannan matakin zai yi mummunar illa kan kasar India saboda takukukamn kasar Venezuela da tuni suka shafe ta.

Kasar India da ta kasance ta uku wajen karfin tattalin arziki a Asiya, na shigo da kashi 80 cikin 100 na danyan man fetur da take bukata.

Kasashen da matakin suka shafa, sun hada da China da India da Japan da Turkiya da Italiya da Girka da Korea ta Kudu da kuma Taiwan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.