Majalisar Dinkin Duniya

Rahoto kan bikin ranar Yan Jaridu ta duniya

'Yan jarida na fuskantar muzgunawa da kisa a yayin gudanar da aikinsu a sassan duniya.
'Yan jarida na fuskantar muzgunawa da kisa a yayin gudanar da aikinsu a sassan duniya. RFI Hausa

UKU ga watan Mayu na kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don gudanar da bikin 'yancin da kare hakkin manema labarai inda ake nazari kan hanyoyin da za a tabbatar da 'yancin Yan Jaridun, tare da sake mara musu baya don gudanar da ayyukansu kamar yadda yarjeniyoyi na kasa da kasa suka tabbatar.Taken Bikin bana dai shi ne “Kafofin yada labarai da Demokradiyya, aikin manema labarai da zabuka a lokacin da ake jirkita labarai”.Daga Maiduguri, wakilinmu Bilyaminu Yusuf ya hada mana rahoto akan wannan rana.