Jarida

'Yan jarida 95 sun rasa rayukansu a bakin aiki

'Yan jarida na fuskantar muzgunawa da kisa a yayin gudanar da aikinsu a sassan duniya
'Yan jarida na fuskantar muzgunawa da kisa a yayin gudanar da aikinsu a sassan duniya RFI Hausa

Yau ita ce ranar ‘Yancin Aikin Jarida da kuma Yada Labarai a Duniya, kuma a cewar Kungiyar Kare ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya, Reporters Sans Frontieres, Afghanistan ce kasa mafi wuyar aiki da kuma muzgunawa ma’aikatan yada labarai a cikin shekarar da ta gabata, yayinda aka kashe jumullar 'yan jarida 95 a bara kadai.

Talla

Kungiyar Tarayyar ‘Yan Jaridu ta Kasa da Kasa, IFJ ta ce, akalla ‘yan jaridu 95 aka kashe a bara a lokacin da suke bakin aikinsu, adadin da ya zarce wanda aka samu a shekarar 2017, amma bai kai adadin da aka samu a shekarun da suka gabata ba, wato lokacin da aka yi ganiyar fama da rikicin Iraqi da Syria.

Kisan da aka yi dan jaridar Saudiya Jamal Khashoggi, na daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankula a bara, lamarin da ya haddasa tsamin dangantaka tsakanin Turkiya da Saudiya, yayinda kasashen duniya suka yi ta tofa albarkacin bakinsu akan lamarin.

Kazalika an kashe wata ‘yar jaridar Birtaniya mai suna Lyra McKee a daidai lokacin da take aika rahoto kan tarzomar da ta barke a Londonderry.

A birnin Paris na Faransa, a wannan rana ta Juma’a za a kaddamar da wani dandali don karrama wasu ‘yan jaridar kasar uku da suka rasa rayukansu a bakin aiki.

‘Yan jaridun dai su ne Ghislaine Dupont da Claude Verlon wadanda aka kashe a kasar Mali, sai kuma Camille Lepage wanda ya hadu da ajalinsa a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Za a gudanar da bikin kaddamar da wannan dandali ne a gaban Shugabar Kafafen Yada Labaran Faransa da ke Yada Shirye-shiryensu da Harsunan Ketare Marie-Christine Saragosse, da kuma shugabar RFI Cécile Mégie.

Ko a kasashen Afrika, Ma’aikatan Yada Labarai sun ci karo da matsaloli da dama a cikin shekarar bara, da suka hada da kamawa da tsarewa yayinda a wasu lokuta har da ma duka.

Uthman Abubakar shi ne Editan jaridan Daily Trust a shiyar arewa maso gabashin Najeriya, a farkon wannan shekara jam’ian tsaro sun kama shi saboda wallafa labari game da yaki da Boko Haram, kuma a yayin zantawarsa da sashen hausa na RFI, ya ce, muzgunawar da ya fuskanta daga hannun jami’an tsaron Najeriya ba za ta hana shi ci gaba da aikinsa na binciko gaskiya da kuma yada ta ga duniya ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ba za a tauye ‘yancin kafafen yada labarai ba a karkashin mulkinsa, yayinda ya jinjina wa ‘yan jaridun kasar kan yadda suke gudanar da ayyukansu a kasar.

Kodayake shugaban ya shawarci ‘yan jaridun da su kara zage dantse wajen kula da dokokin aikin jarida kamar yadda sanarwar da mai taimaka masa na musamman a fannin kafafen yada labarai Femi Adesina ya fitar ta bayyana.

Kwararru a ilimin Jarida da suka hada da shehannan malaman jami’o’i sun shawarci ‘yan jaridu da su rika tabbatar da tushen labarinsu kafin yadawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI