Isra'ila- Falasdinu

Isra'ila ta dauki mataki mai tsauri kan Falasdinawa

Daya daga cikin rokokin da aka cilla su daga zirin Gaza
Daya daga cikin rokokin da aka cilla su daga zirin Gaza REUTERS/Bashar Talib

Kasar Isra’ila ta dakile kayayyaki da mutanen da ke tsallakawa ta hanyar zirin Gaza, yayinda kuma ta rufe yankin da masu Su ke hada-hadarsu a matsayin martani ga makaman rokar da Falasdinu ta harba mata.

Talla

Ma’aikatar Tsaron Isra’ila da ke kula da yankin, ta ce, wannan matakin da suka dauka a zirin na Gaza zai ci gaba da aiki har sai Baba-ta-gani.

Isra’ila ta ce, Falasdinawa sun cilla mata akalla makaman na roka har guda 150, lamarin da ya sa ta kaddamar da hare-haren jiragen sama a matsayin ramuyar gayya.

Tuni Kungiyar Kasashen Turai ta bukaci gaggauta kawo karshen harbe-harben rokokin, yayinda ta goyi bayan yunkurin kasar Masar da Majalisar Dinkin Duniya na kwantar da hankula tare da kare rayukan fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.