Isra'ila- Palestine

Isra'ila ta kashe kwamandan Hamas a Gaza

Ana ci gaba da daridarin makomar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu bayan sabon rikicin da ya barke a tsakaninsu
Ana ci gaba da daridarin makomar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu bayan sabon rikicin da ya barke a tsakaninsu REUTERS/Mohammed

Hukumomin Zirin Gaza sun tabbatar da kashe kwamandan Falasdinawa a hare-haren ramako da Isra’ila ta kaddamar kan yankin.

Talla

Ma’aikatar kiwon Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa, an kashe Hamad al-Khadori mai shekaru 34 da ya kasance daya daga cikin kwamandojin Kungiyar Hamas.

Rikicin tsakanin bangarorin biyu ya dada kazancewa a karshen mako, yayinda Isra’ila ta ce, Falasdinawan sun harba mata rokoki sama da 450, abinda yasa ta mayar ta martanin hare-haren jiragen sama.

Tuni Kungiyar Kasashen Turai ta bukaci gaggauta kawo karshen harbe-harben rokokin, yayinda ta goyi bayan yunkurin kasar Masar da Majalisar Dinkin Duniya na kwantar da hankula tare da kare rayukan fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.