Libya-Turai

Fayez Sarraj na neman goyon kasashen Turai kan Libya

Firaministan Italiya, Giuseppe Conte da  shugaban gwamnatin Libya Fayez al-Sarraj a birnin Rome
Firaministan Italiya, Giuseppe Conte da shugaban gwamnatin Libya Fayez al-Sarraj a birnin Rome Filippo MONTEFORTE / AFP

Firaministan Italiya, Giuseppe Conte ya yi gargadi game da daukar matakin soji akan Libya, a daidai lokacin da shugaban gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan kasashen duniya, Fayez Sarraj ke fara ziyara a nahiyar Turai. Babbar manufar wannan ziyarar ita ce neman agajin kasashen Turai dangane da hare-haren da Khalifa Haftar ke kaddamawar a kasar ta Libya.

Talla

Shugabannin biyu sun kwashe kimanin mintina 90 suna tattaunawa da juna a birnin Rome kamar yadda kafafen yada labaran Italiya suka rawaito, amma ba a bayyana wa jama’a cikakken abinda suka zanta akai ba.

Sai dai a gefen taronsu, Conte ya ce, za a dauki matakin soji a Libya ne muddin aka ci gaba da samun asarar rayuka, amma duk da haka, ayyukan sojin ba za su tabbatar da zaman lafiya a kasar ba a cewarsa.

Fayez Sarraj dai na bukatar taimakon kasashen Turai game da farmakin da Khalifa Haftar ke kaddamarwa a birnin Tripoli, in da har ma ya bukaci dakarunsa da su murkushe dakarun gwamnatin kasar.

Bayan ganawarsa da Conte, Sarraj zai kama hanyar birnin Berlin a yau Talata domin tattaunawa da shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel kafin kuma ya sake daukar hanyar birnin Paris don zantawa da shugaban Faransa Emmanuel Macron a gobe Laraba, sannan akwai yiwuwar ya nausa can Birtaniya daga Faransa.

Sai dai ziyararsa a Faransa na zuwa ne bayan gwamnatinsa ta rikon kwarya ta zargi hukumomin Paris da shigar da siyasa wajen nuna goyon baya kan hare-haren da dakarun Haftar suka kaddamar a Tripoli a ranar 4 ga watan Afrilu.

Italiya wadda ta yi wa Libya mulkin mallaka, na kan gaba wajen goyon bayan gwamnatin rikon kwaryar kasar, yayinda ta yayata kiran da Angela Merkel ta yi na ganin kasashen Turai sun dauki matakin bai-daya wajen warware rikicin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI