Palestine-EU

Falasdinu ta bukaci EU ta shiga tsakaninta da Isra'ila

Falasdinawa sun ce, sun fi amincewa da Kungiyar Tarrayar Turai a matsayin mai shiga tsakani wajen magance rikicinsu da Isra'ila, yayinda suka bayyana tababa akan sahihancin shiga tsakanin Amurka
Falasdinawa sun ce, sun fi amincewa da Kungiyar Tarrayar Turai a matsayin mai shiga tsakani wajen magance rikicinsu da Isra'ila, yayinda suka bayyana tababa akan sahihancin shiga tsakanin Amurka (Montage : RFI)

Al’ummar Falasdinawa sun bukaci Kungiyar Tarayyar Turai da ta karbi ragamar tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu da Isra’ila muddin shirin Amurka ya yi wasti da batun kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yancin kai.

Talla

Ana dakon gwamnatin shugaba Donald Trump ta kaddamar da shirinta a cikin wannan wata, sai dai tuni al’ummar Falasdinawa suka yi watsi da shirin saboda yadda ya dauki bangarancin yi wa Isra’ila alfarma.

A yayin ganawa da manema labarai labarai, Jakadan Falasdinu, Riyad Mansour ya ce, ya bukaci hukumomin kasashen Turai a wani zama da suka yi tare a a birnin Brussels cewa, su karbe ragamar shirin zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra’ila, sannan kuma su hana Amurka yin kane-kane a cikin shirin.

Jakadan ya ce, za su yi murna matuka muddin aka samu sama da kasa guda wajen shiga tsakani a rikicin Falasdinu da Isra’ila.

Kazalika, Falasdinawan sun bukaci kasashen Turai musamman ma Faransa da Italiya da Sapain da Portugal da Ireland da Belgium da Luxembourg da su amince da Falasdinu a matsayin kasa guda mai cin gashin kanta.

Kudurin Majalisar Dinkin Duniya dai, ya bukaci samar da kasar Falasdinu daban da kuma kasar Isra’ila daban a matsayin hanyar magance rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu.

Kudurin na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma jaddada cewa, dole ne bangarorin biyu su amince da wannan matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.