Isa ga babban shafi
Iran-AMurka

Nukiliya: Kasashen duniya sun yi raddi kan matakin kasar Iran

Shugaban Iran Hassan Rohani a cibiyar makamashin nukiliyar kasar
Shugaban Iran Hassan Rohani a cibiyar makamashin nukiliyar kasar AFP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman | Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Manyan kasashen duniya, musamman wadanda abin ya shafa kai tsaye, sun maida martani kan matakin da Iran ta dauka, na daina aiki da wasu kudurorin yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen a shekarar 2015.

Talla

Yayin bayyana matakin, Iran ta ce ba za ta janye matakin da ta dauka ba, har sai manyan kasashen da ke cikin yarjejeniyar sun dakile tasirin takunkuman da Amurka ta sake kakaba mata.

Shugaban Iran, Hassan Rouhani yace kasar za ta sake janyewa daga karin wasu bangarorin yarjejeniyar nukiliyar nan da kwanaki 60, muddin Birtaniya, China, Faransa, Jamus da kuma Rasha suka gaza dankwafar da sabbin takunkuman Amurka da suka soma aiki akanta.

Jamus ce ta soma maida martani kan matakin na Iran, ta hannun kakakinta Steffen Seibert, inda da bukaci kasar ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar baki dayanta kamar yadda itama Jamus din ke yi. Yayinda ita kuma Birtaniya ta bayyana hukuncin na Iran a matsayin abin da bai dace ba, zalika ta kaucewa sake daukar makamancinsa a gaba.

A nata bangaren, China bayyana adawa ta yi da sabbin takunkuman da Amurka ta kakabawa Iran, sai dai ta bukaci sauran takwarorinta su ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar.

Rasha da ta jaddada matsayinta kan kare yarjejeniyar, tayi amfani da kakkausan harshe wajen sukar matakan Amurka na kuntatawa kasar da nufin tilasta rushe yarjejeniyar nukiliyar a kuma tsara sabuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.