Isa ga babban shafi

Hukumar kula da abinci ta koka da karuwar yunwa a sassan duniya

Wasu motocin agajin abinci karkashin shirin Majalisar Dinkin Duniya na yaki da yunwa
Wasu motocin agajin abinci karkashin shirin Majalisar Dinkin Duniya na yaki da yunwa Reuters
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 min

Hukumar Kula da ayyukan noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana cigaba da samun karuwar yunwa a kasashen da ke Gabashin Asia da Arewacin Afirka, inda yanzu haka ake da mutane sama da miliyan 52 da ke fama da rashin abinci mai gina jiki sakamakon tashe tahsen hankula.

Talla

Sanarwar da hukumar kula da ayyukan noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar ya bayyana cewar tashe tashen hankulan da ake samu wadanda ke cigaba da yaduwa tun daga shekarar 2011 na yiwa Yankunan barazana kan shirin sun a korar yunwa.

Rahotan kungiyar yace mutane sama da miliyan 52 na fama da tsananin rahsin abinci mai gina jiki, kuma kashi biyu bisa uku daga cikin sun a zama ne a yankunan da ake fama da tashin hankali.

Hukumar ta bayyana kasashen da lamarin yafi kamari da suka hada da Iraqi da Libya da Sudan da Syria da kuma Yemen, wanda yakin da ake gwabzawa a cikin ta yayi sanadiyar hallaka dubban mutane.

Rahotan ya kuma ce, bayan rikice rikicen, matsalar karuwar jama’a na dada kamarin lamarin, sakamakon raguwar arzikin da ake da shi.

Domin shawo kan matsalar, Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci inganta harkar noma da samar da abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.