Iraqi-IS

Iraqi ta hukunta mayakan IS 514 da suka shiga Syria yaki daga Turai

Wasu mayakan IS a birnin Mosul
Wasu mayakan IS a birnin Mosul AHMAD AL-RUBAYE / AFP

A kasar Iraki, an yanke hukunci akan magoya bayan kungiyar IS ‘yan asalin kasashen ketare sama da 500 daga bara zuwa bana kamar dai yadda wata sanarwa da mahukuntan kasar suka fitar ke nunawa.

Talla

Kotun kolin kasar ce ta fitar da wadannan alkalumma da ke tabbatar da cewa an yanke hukuncin dauri a kan mujahidai ‘yan asalin kasashen waje 514, sai wasu 202 ke jiran a yanke masu hukunci nan gaba yayin da aka sallami wasu 11.

Sanarwar ta ce wadanda aka yanke wa hukuncin mayaka ne da suka fito daga kasashen duniya daban daban kuma an kama su ne a fagen daga, kuma an share tsawon watanni shida ana bincike kafin tabbatar da laifufukansu.

An yanke hukunce-hukunce a matakai daban-daban har da daurin raida-rai, yayin da bayanai suka tabbatar da cewa akwai wani banfaranshe Lahcen Ammar Gueboudj mai shekaru 58 da aka yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai.

A shekara ta 2017 ne Iraqi ta sanar da murkushe mayakan na IS, inda suka dauke tungarsu zuwa Syria, inda a can ma rahotanni ke cewa akwai mayakan jihadi ‘yan asalin kasashen sama da dubu 1 da kuma ‘yaya da matayensu sama da dubu 9 a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.