Isra'ila-Falasdinawa

Isra'ila ta janyewa Falasdinawa dokar hana kamun kifi

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Abir Sultan/Pool via REUTERS

Isra’ila ta janye dokar haramcin kamun kifi da ta kakabawa, kananan jiragen ruwan Falasdinawa da ke sana’ar suu a gabar ruwan da ke kan iyakarta da yankin Gaza.

Talla

Matakin dage haramcin kamun kifin, wani bangare ne na soma aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da bangarorin suka cimma, bayan da a makon da ya gabata, Jiragen yakin Isra’ila suka kai wa cibiyoyin mayakan kungiyar Islamic Jihad da ke gaza farmaki, a matsayin martini kan harba makaman roka akalla 250 da suka yi cikin Isra’ilar.

A baya dai sojin ruwan Isra’ila kan bude wuta kan Falasdinawan da ke sana’ar ta ta kamun kifi a duk lokacin da suka ketara kan iyakar ruwan da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.