Gwajin makamin Korea ta Arewa ba zai shafi tattaunawarmu ba- Trump
Wallafawa ranar:
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce matakin kasar Korea ta Arewa na sake gwajin wasu makaman nukiliya da kuma karfafa sashen makamin ba zai gurbata tattaunawarsa da Kim Jong Un kan ganin kasar ta lalata makamanta ba.
A shekaran jiya Alhamis ne Korea ta Arewan ta yi gwajin wasu makamai masu linzami da ke cin dogon zango karon farko cikin watanni 18 tun bayan fara tattaunawarta da Amurka, yayinda kuma ta sha alwashins ake wani gwajin a yau Asabar, wanda ke zuwa bayan kame mata wasu jiragen ruwa makare da Kwal da Amurka ta yi cikin makon nan.
Sai dai duk da hakan Donald Trump a zantawarsa da manema labarai ya ce ko kadan Korea ta Arewan ba ta saba ka’idar tattaunawarsu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu