Pompeo zai gana da Putin kan rikicin kasar Venezuela
Wallafawa ranar:
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya kama hanyar zuwa Rasha don ganawa da shugaba Vladimir Putin a wani mataki da ke matsayin godiya ga alkawarinsa na kin yin katsalandan a harkokin siyasar Venzeuela, bayan da a baya aka zarge shi da mara baya ga shugaba Nicolas Maduro da Amurka ke kokarin hambararwa.
A ranar Talata mai zuwa ne za a yi ganawar tsakanin Pompeo da Putin wadda aka tsara za ta gudana a Sochi wadda kuma za ta zamo irinta ta farko tun bayan ganawar Trump da Putin da ta gudana a Helsinki cikin watan Yulin bara da ta haddasawa Trump tarnaki a cikin gida.
A ranar 3 watan Mayun da mu ke ciki ne Trump ya yi wata waya tsakaninsa da Putin wadda ta debe su sa’o’i da dama, inda yayin tattaunawar Putin ya tabbatarwa shugaban na Amurka cewa ba zai tsoma baki a rikicin siyasar na Venezuela ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu