Faransa

Faransa ta karrama sojinta da aka kashe a Afrika

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron a wurin bikin karrama sojin kasar da suka mutu a Benin
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron a wurin bikin karrama sojin kasar da suka mutu a Benin REUTERS/Philippe Wojazer/Pool

Kasar Faransa ta karrama kwamandojin sojinta na musamman da suka rasa rayukansu a yayin samamen ceto baki ‘yan yawon bude ido da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su akan iyakar kasar Benin da Burkina Faso a makon jiya.

Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya jagoranci bikin karramawar karshe ga Cedric de Pierrepont mai shekaru 33 da Alain Bertoncello mai shekaru 28 da suka rasa rayukansu a yankin Sahel na Afrika a yayin kubutar da wasu mutane da ‘yan bindiga suka sace.

Dandazon jama’a sun saje da sojojin Faransa da suka hada da jami’an kwana-kwana da wasu zaratan dakaru a tattakin da suka yi zuwa can wani ginin karni 17a birnin Paris, yayinda ayarin motoci ke dauke da akwatinan gawar sojin biyu da aka kashe.

A yayin gabatar da jawabinsa cikin yanayin tausayi, shugaba Emmanuel Macron ya ce, Faransa kasa ce da ba ta mancewa da ‘ya’yanta duk rintsi kuwa.

Macron ya kara da cewa, sun halarci bikin na yau ne domin jaddada cewa, ba za su taba karaya ba a irin wannan yakin da ya yi sanadiyar mutuwar sojin na Faransa.

Akwai dai Faransawa guda biyu cikin mutanen hudu da aka ceto daga hannun ‘yan bindigan kuma an sace su ne a ranar 1 ga watan Mayu a daidai lokacin da suke kan yawon bude ido a wani gandun-daji da ke Jamhuriyar Benin, kusa da kan iyaka da Burkina Faso.

Sai dai Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean Yves Le Drien ya caccaki Faransawan biyu da aka kubutar saboda yadda suka yi kasadar ziyartar yankin na Afrika mai hadari.

Sauran mutanen biyu sun fito ne daga Amurka da kuma Korea ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.