Cyber Crime

'Yan sanda sun kama barayin da ke sata a Kwamfuta

Masu kutsen sun ce akalla Dala miliyan 100 daga asusun mutane dubu 41
Masu kutsen sun ce akalla Dala miliyan 100 daga asusun mutane dubu 41 Pixabay

Jami’an ‘Yan sandan Amurka da na Kasashen Turai sun yi nasarar cafke wasu masu kutsen kwamfuta da suka yi amfani da manhajar Malware wajen sace Dala miliyan 100 a wasu kasashen duniya.

Talla

Tuni kasashen Georgia da Maldova da Ukraine da Amurka suka gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a wannan gagarumin farmakin sata ta hanyar kwamfuta, inda a Amurka ake tuhumar Rashawa biyar da suka tsere kamar yadda Hukumar ‘Yan sandan Kasashen Turai ta sanar.

Masu kutsen sun sace Dala miliyan 100 ne daga mutane akalla dubu 41 da suka hada da attajiran ‘yan kasuwa da cibiyoyin hada-hadar kudade.

Masu kutsen sun yi amfani da wata muguwar manhajar Malware domin daburta kwakwaluwar kwamfutocin jama’a kafin sace bayanansu na asusun ajiyar bankunansu, sannan daga bisani suka wawure kudadensu cikin sauki.

An dai karkata akalar kudaden ne zuwa Amurka da wasu asusun bankuna.

Babban lauyan gwamnatin Amurka da ke kula da yankin Pennsylvania, Scot Brady, ya bayyana kokarin jami’an ‘yan sanda na cafke masu kutsen a matsayin wata bajintar hadin guiwa da ba a taba ganin irinta ba tsakanin kasashe.

An cafke jagoran masu kutsen ne a kasar Georgia, inda aka bayyana shi da suna Alexandre Konovolov mai shekaru 35, dan asalin kasar Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI