Najeriya-Afrika-Duniya

Dangote ya zama na 11 a jerin fitattun mutane 50 a duniya

Attajirin nahiyar Afrika, Aliko Dangote Aliko Dangote.
Attajirin nahiyar Afrika, Aliko Dangote Aliko Dangote. REUTERS/Denis Balibouse

An bayyana attajirin nahiyar Afrika Aliko Dangote, a matsayin mutum na 11 daga cikin fitattun jagororin duniya 50, da suka fi kwazo da kuma tallafawa jama'a a wannan shekara.

Talla

Mujallar Fortune mai nazari kan sha’anin kasuwanci da sauran al’amuran gudanarwa na kasa da kasa da ke birnin New York a Amurka ce ta gudanar da binciken kan mutanen da ta zabo tare da karrama su da matsayin da ta wallafa.

Rahoton da mujallar ta Fortune ke fitarwa a kowace shekara, na maida hankali ne kan sha’anin kasuwancin da dai-daikun mutane suka kafa, da kuma yadda suka yi amfani da damarsu wajen taimakawa yankunansu ta hanyar ingantawa jama’a rayuwa da kuma saukaka musu al’amura ta fannoni daban daban.

Karo na farko kenan da mujallar ta sanya Aliko Dangote cikin jerin fitattun jagorori a duniya da suka taimakawa jama’arsu matuka, kuma daya daga cikin dalilan da suka baiwa Attajirin na nahiyar Afrika wannan nasara shi ne gidauniyar da ya kafa da ke bada tallafin rage yawan rayukan mutanen da ke salwanta a dalilin rashin abinci mai gina jiki, da kuma fama da nau’ikan cutuka da ke zama annoba, sai kuma tallafawa ilimin kananan yara, da kuma ragewa jama’a radadin talauci.

Wasu daga cikin manyan mutanen 50 da mujallar Fortune ta bayyana a matsayin wadanda ke sahun gaba a fagen tallafawa al’umma sun hada da Bill Gates a matsayin na farko, Fira Ministar kasar New Zealand Jacinda Arden, sai kuma Robert Mueller na ma’aikatar shari’ar Amurka a matsayi na uku.

A shekarar 2018 mujallar Time ta bayyana Aliko Dangote a matsayin daya daga cikin mutane 100 a duniya da suka fi tasiri kan rayuwar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.