Gawar Tshisekedi za ta koma Congo bayan shekaru biyu a Belgium
Wallafawa ranar:
Iyalan tsohon shugaban 'yan adawan Jamhuriyar Demokiradiyar Congo, Etienne Tshisekedi sun bayyana cewar za a mayar da gawarsa gida daga kasar Belgium shekaru biyu bayan mutuwarsa a can.
Etienne Tshisekedi wanda shi ne mahaifin shugaba Felix Tshisekedi da aka rantsar a matsayin shugaban kasa a wannan shekara, ya rasu bayan ya gamu da rashin lafiya a Belgium yana da shekaru 84, amma rikicin siyasar kasar ya hana a mayar da gawarsa gida.
Dan uwansa, Arch Bishop Gerard Mulumba ya ce, ranar 30 ga watan nan za a mayar da gawar gida, kana a yi masa jana’iza ranar 1 ga watan Yuni.
Marigayin ya taka rawa a fagen siyasar Jamhuriyar Dimokradiyar Congo duk da cewa, bai samu nasarar zama shugaban kasa ba, yayinda ya kasance kan gana wajen sukar mulkin kama-karya na Mobuto Sese Seko.
Bayan fitowarsa daga gidan yari a shekarar 1982, marigayin ya jagoranci kafa jam'iyyar Union for Democracy and Social Progress, wadda ta zama babbar jam'iyyar adawa a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu