Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa-Amurka

Koriya ta Arewa ta yi wa Amurka gargadi kan jirgin ruwanta

Jirgin ruwan dakon-kaya na Koriya ta Arewa da Amurka ta kama
Jirgin ruwan dakon-kaya na Koriya ta Arewa da Amurka ta kama Reuters/路透社
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris
1 Minti

Kasar Koriya ta Arewa ta gargadi Amurka game da abinda ka iya faruwa biyo bayan kama mata jirgin ruwanta na dakon-kaya.

Talla

Jakadan Koriya a Majalisar Dinkin Duniya, Kim Song ya shaida wa manema labarai cewar, kasarsa na sa ido kan matakan da Amurka ke dauka sakamakon kama jirgin mai suna Wise Honest.

Jakadan ya bukaci Amurka ta gaggauta sakin jirgin ruwan ko kuma ta zauna ta yi nazarin abinda zai biyo baya kan lamarin.

A ranar 9 ga watan nan Amurka ta sanar da kama jirgin ruwan saboda zargin da take yi cewar ana amfani da shi wajen safarar gawayi, lamarin da ya saba wa dokokin Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.