Amnesty ta bukaci Mauritania ta gaggauta sakin wasu 'yan Jaridu 2

Tambarin kungiyar Amnesty International
Tambarin kungiyar Amnesty International Amnesty

Kungiyar Amnesty International ta bukaci gwamnatin Mauritania da ta gaggauta sakin wasu 'yan Jaridu biyu da suka yi suna da aka tsare watanni biyu kenan saboda labaran da suka wallafa a shafunan sun a intanet.

Talla

Amnesty tace an kama mutanen Abderrahmane Waddady da Cheik Ould Jiddou a karshen watan Maris saboda zargin da suka yi na cin hanci cikin manyan jami’an gwamnati.

Kine Fatim Diop, Daraktan kungiyar a Yankin Afirka ta Yamma ya ce tsare su ba bisa ka’ida ba da gwamnatin Mauritania ta yi da kuma tuhumar da ake musu ya nuna yadda Mauritania ke kokarin hana fadin albarkacin baki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.