Taiwan

Taiwan ta amince da auren jinsi

Bukin auren jinsi na farko a Thailand
Bukin auren jinsi na farko a Thailand REUTERS/Tyrone Siu

Kasar Taiwan ta bi sahun wasu kasashen duniya da ke halatta auren jinsi, inda ta daura auren wasu karti biyu a wani gagarumin buki a babban birnin Taipei.

Talla

A harabar da aka daura auren, babu masaka tsinke kuma a karon farko kenan da ake daura irin wannan auren tun bayan da wakilan majalisar kasar suka zartas da dokar halatta auren jinsin.

Bayanai sun nuna cewa, shekaru kusan 30 kenan da masu hankoron ganin an halatta auren jinsin a Taiwan ke neman a biya musu bukatarsu.

Matakin na zuwa ne duk da cewa ‘yan adawa sun hau kujeran naki.

Wasu tulin masu kaunar a daura masu auren jinsin na ta rige-rigen zuwa ofishin gwamnati da ke kula da lamarin don gabatar da kansu da zummar yi musu rajista.

Ma'aurata mazansu da mata na ta tsotsan bakin juna da rungume juna a bainal jama’a, bayan halartar bukin daura auren na farko da aka yi.

Wata mace mai suna Huang Mei-yu, kusan ta zuba ruwa a kasa ta sha, inda take cewa, yanzu iyayenta sa daina matsa mata da ta auri namiji, tunda dai gwamnati ta san da zamansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI