Majalisar Dinkin Duniya

Za a kashe Dala miliyan 363 wajen yaki da cin zarafin mata

Wasu mata a Faransa na zanga-zangar cin zarafin 'yan uwansu mata a wasu kasashen duniya
Wasu mata a Faransa na zanga-zangar cin zarafin 'yan uwansu mata a wasu kasashen duniya REUTERS/Jean-Paul Pelissier

Kasashen duniya sun yi alkawarin bayar da Dala miliyan 363 domin yaki da masu cin zarafin mata lokacin da ake gudanar da ayyukan jinkai a wuraren da ake fama da tashin hankali a duniya baki daya.

Talla

Majalisar Dinkin Duniya da ta shirya taron da aka yi a Oslo ta ce, kasashe 21 sun yi alkawarin bada nasu agajin kudaden a shekarar 2019 da 2020.

Mark Lowcock, Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar da ke kula da ayyukan jinkai ya ce, ana bukatar Dala miliyan 660 a cikin wannan shekara domin yaki da yadda ake cin zarafin maza da mata, lamarin da ke lalata al’ummomi da kuma rayuwar wadanda aka ci zarafinsu.

Norway da ta karbi nauyin taron ta bada Dala miliyan 115.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.