Amurka

Amurka ta sayar wa kasashen larabawa makamai saboda Iran

Shugaban Amurka Donald Trump yana yi wa manema labarai jawabi kan matakin tura sojin kasar zuwa yankin Gabas ta Tsakiya
Shugaban Amurka Donald Trump yana yi wa manema labarai jawabi kan matakin tura sojin kasar zuwa yankin Gabas ta Tsakiya 路透社。

Gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amurka ta yi gaban kanta wajen sayar da makamai na Dala biliyan 8.1 ga Saudiya da wasu kasashen Larabawa ba tare da samun amincewar Majalisar Dokokin Kasar ba kafin daukar wannan mataki, tana mai bayyana barazana daga Iran a matsayin babban dalili.

Talla

Sakataren Harkokin Wajen kasar, Mike Pompeo ya bayyana cewa, gwamnatin Trump za ta shawo kan Majalisar Dokokin domin amincewa da aika wasu makamai har guda 22 ga Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Jordan.

‘Yan Majalisar Dokokin Amurka na fargabar cewa, sayar da makaman ga wadannan kasashe ka iya haifar da kisan fararen hula a Yemen.

Sai dai gwamnatin Trump ta dauki matakin ne saboda barazanar da ke kunno kai daga kasar Iran a cewarta.

A bangare guda, Amurkar ta sanar da shirinta na tura sojoji dubu 1 da 500 zuwa yankin Gabsa ta Tsakiya a matsayin martani kan abinda Ma’aikatar Tsaro ta Pentagon ta kira da hare-haren Iran.

Shugaba Donald Trump ne ya amince da matakin tura dakarun, inda yake cewa, suna fatan samun kariya a yankin Gabas ta Tskiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.