Fursunoni 25 sun mutu a rikicin gidan yarin Venezuela
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Akalla fursunoni 25 sun rasa rayukansu, yayinda jami’an ‘yan sanda 20 suka jikkata sakamakon rikicin da ya barke a wani gidan yari da ke kudancin kasar Venezuela.
An samu tashin hankalin ne bayan wasu jami’an ‘yan sanda na musamman sun yi kokarin kubutar da wasu baki da shugaban mazauna gidan yarin ya yi garkuwa da su.
Kungiyar da ke kare hakkin fursunoni a kasar ta ce, fursunonin nada makamai a hannunsu, inda suka harbi jami’an ‘yan sandan, sannan kuma suka tayar da wasu kanana bama-bamai.
Rahoton jami’an ‘yan sanda ya ce, shugaban fursunonin, Wilfredo Ramos na cikin wadanda aka kashe a rikicin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu