Isa ga babban shafi
Salvador

An rantsar da Shugaban kasar Salvador

Nayib Bukele Sabon Shugaban kasar Salvador
Nayib Bukele Sabon Shugaban kasar Salvador REUTERS/Tom Brenner
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

A yau asabar aka rantsar da sabon Shugaban kasar Salvador Nayib Bukele mai shekaru 38 da ya yi nasara a zagayen farko tareda lashen zaben Shugabancin kasar da kuri’u kashi 53 cikin dari da aka kada a zaben watan Fabrairu.

Talla

Kasar na daga cikin kasashen da cin hantsi da rashawa ya yiwa katutu, Shugabanin kasashen da suka taba rike muakamin shugabanci na fuskantar tuhuma biyo bayan samun su da laifin azurta kan su ta hanyar da ba ta dace ba.

A wannan bikin da ya gudana babban birnin kasar San Salvador, dubban yan kasar suka fito domin sake jaddada goyan bayan su zuwa canji, yayinda manazarta ke bayyana cewa kalubalen dake gaban sabon Shugaban kasar za su hada da yaki da cin hantsi da karbar rashawa daga jami’an gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.