Ghana- Canada

An Sace 'Yan Kasar Canada 2 A Ghana

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo rfi

'Yan Sanda a kasar Ghana sun sanar da  sace ‘yan kasar Canada biyu a filin wasannin kwallon lambu dake Kumasi na kasar Ghana.

Talla

‘Yan kasar ta Canada biyu na ayyukan agaji ne a kasar Ghana kuma suna da shekaru 19 da 20.

Da yammacin Talata aka sace su a garin Kumasi,  gari na biyu wajen girma a Ghana mai tazaran kilomita 200 arewa maso yammacin birnin Accra babban birnin kasar.

Kwamishinan ‘yan sandan David Eklu ya fadi cikin wata sanarwa cewa dukkaninsu mata ne.

Ya yi bayanin cewa ‘yan Sanda na ci gaba da gudanar da cikakken bincike domin gano inda 'yan matan suke don kubutar da su.

Ya ce ‘yan matan na cikin wata mota da suka yi haya tare da rakiyar wata mace ‘yan kasar Canada amma ba’a tafi da maccen ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI