Venezuela

Venezuela ta rufe ofishoshin jakadanci dake Canada

Nicolas Maduro  Shugaban Venezuela
Nicolas Maduro Shugaban Venezuela ©REUTERS/Ivan Alvarado

Kasar Venezuela ta sanar da aniyar ta na rufe kananan ofishoshin jakadancin kasar dake kasar Canada biyo bayan matakin hukumomin Canada na rufe ofishin jakadancin kasar dake birnin Caracas.

Talla

Gwamnatin Venezuela ta bayyana cewa a duk fadin kasar ta Canada, ofishin jakadancin ta daya cillo dake birnin Ottawa zai ci gaba da aikin sa.

Mako daya kenan da hukumomin Canada suka dau matakin rufe ofishin jakadancin su,bisa dalilan cewa Shugaban kasar Nicolas Maduro ya hanawa wasu jakadun Canada takardun aiki a kasar.

Matakin rufe ofishoshin jakadancin Venezuela a Canada na zuwa ne a wani lokaci da kasashen Duniya ke ci gaba da kira zuwa Shugaba Maduro na kawo sassauci ga shugabancin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI