Isa ga babban shafi
India

Kotun India ta samu wasu kattai da laifin yi wa Musulma fyade

Kananan yara na fuskantar barazanar fyade a India
Kananan yara na fuskantar barazanar fyade a India REUTERS/Sivaram V TPX IMAGES OF THE DAY
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Kotun India ta samu wasu kattai shida da laifin yin fyade da kuma kashe wata karamar yarinya Musulma ‘yar shekara takwas a bara, lamarin da ya haddasa tayar da jijiyoyin wuya tsakanin mabiya addinan Hindu da Islama a kasar.

Talla

Bayanan kotun sun bayyana cewa, yarinyar wadda aka danganta ta Fulanin India, an sace ta ne a yayin da take kiwon dawaki, inda aka kai ta wani kauye da ke yankin Kathua a ranar 10 ga watan Janairun bara, sannan kuma aka yi mata fyade babu kakkautawa bayan daddaka mata maganin barci a wata Mujami’ar mabiya addinin Hindu.

Kazalika an yi amfani da kulki wajen azabtar da yarinyar, sannan kuma aka makure wuyanta har lahira.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa, an aikata wannan danyen aikin ne domin jefa tsoro a zukatan al’ummar Fulanin India makiyaya don ganin sun fice daga yankin.

Akwai yiwuwar mutanen da suka yi wa yarinyar fyade su fuskanci hukuncin kisa ko kuma akalla daurin rai da rai. Kodayake, lauyen da ke kare su ya ce, za su daukaka kara.

Gwamnatin India ta samar da dokar kisa kan masu yi wa kananan yara fyade ne biyo bayan ta’azzarar matsalar a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.