Palestine

Falasdinu ta bukaci Larabawa sun kaurace wa taron Amurka

Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas REUTERS/Carlo Allegri

Gwamnatin Falasdinu ta bukaci kasashen Masar da Jordan da su kaurace wa taron da Amurka za ta jagoranta a cikin wannan watan a Bahrain da zummar sasanta rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Talla

Kasar Amurka ta bayyana taron a matsayin wanda zai habbaka tattalin arzikin Falasdinu, kuma hakan wani bangare ne na yunkurin magance tankiya tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

Shugabannin Falasdinawa da ke da aniyar kauracewa taron na ranar 25-26 ga watan Yuni, sun ce, shirin zaman lafiyar, ya ci karo da manufofinsu na kafa kasarsu mai cin gashin kanta.

Ana dai ganin cewa, rawar da kasashen Masar da Jordan za su taka a wannan taro nada matukar muhimmanci, lura da cewa, sun dade suna tsoma baki wajen sansanta rikici a yankin Gabas ta tsakiya, yayinda kuma, su kadai ne kasashen Larabawa da ke da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanisu da Isra’ila.

Sai dai mahukuntan Falasdinu ta bakin kakakinsu, Ibrahim Melhem, sun bukaci daukacin aminansu da zu kaurace wa taron, inda suka ce, halartar taron zai yada gurguwar fahimtar cewa, akwai rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen Larabawa dangane da shirin zaman lafiyar da gwamnatin Donald Trump ta bullo da shi.

A bangare guda, Firaministan Falasdinu, Mohd. Shtayyeh da ke mgana a gaban Hukumar Kwadago ta Duniya a birnin Geneva, ya ce, Falasdinawa manoma sun zama kaskantattu saboda yadda filayen da ke Gabar Yamma ga Kogin Jordan ke karkashin ikon isra’ila, lamarin da ya ce, ya dakile ci gaban Falasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.