Hong Kong

Zanga-zangar Hong Kong ta zama tarzoma

Jami'an 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da shirin gwamnatin Hong Kong kan tasa keyar masu laifi zuwa China domin fuskantar hukunci
Jami'an 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da shirin gwamnatin Hong Kong kan tasa keyar masu laifi zuwa China domin fuskantar hukunci 路透社

Zanga–zangar da ake yi a Hong Kong kan adawa da shirin tasa keyar masu laifi zuwa China domin fuskantar shari'a, ta rikide zuwa tarzoma, yayin da Birtaniya ke kira ga hukumomin Hong Kong da su saurari korafin al’umma.

Talla

Tarzomar ta barke ne a yayinda ‘yan sanda ke kokarin hana masu zanga–zangar shiga harabar Majalisar Dokokin Hong Kong, inda dubun-dubatan mutane suka toshe muhimman hanyoyi.

‘Yan sandan sun yi amfani hayaki mai sa hawaye da harsashen roba da kulake don tarwatsa masu zanga-zangar da ke sanye da bakaken tufafi, wadanda akasarinsu matasa ne da dalibai.

Wannan tarzoma ta ranar Laraba ta ja hankalin Birtaniya, wadda a shekarar 1997 ta bai wa Honk Kong ‘yancin cin gashin kai bayan yi mata mulkin mallaka, inda Sakataren Harkokin wajenta, Jeremy Hunt, ya yi kira ga dukkan bangarori da su kwantar da hankalinsu.

A wani sakon bidiyo, shugabar gwamnatin Hong Kong, Carrie Lam ta caccaki masu zanga–zangar, tana mai bayyana tarzomar da ta biyo baya a matsayin wani shiryanyen al'amari,

Lam ta ce, a bayyane yake ba zanga-zangar lumana ake gudanarwa ba, an shirya ne a tada tarzoma ta wajen karya doka da oda, kuma ba za a lamunci haka ba a wannan zamani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.