Guatemala ta cafke 'yan ciranin da ke kokarin tsallakawa Amurka
Wallafawa ranar:
Jami’an ‘yan sandan Guatemala sun sanar da kame wasu ‘yan cirani 24 da suka fito daga kasashen Haiti da Guinea a kokarinsu na tsallakawa Amurka ta barauniya hanya, ta hanyar amfani iyakar kasar daga arewaci.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Pablo Castillo ya bayyana cewa kamen ya biyo bayan wani aikin sintiri da suka gudanar akan hanyoyin da suka hada yankunan kasar, wanda ta nan ne bakin hauren ke samun damar karya doka tare da tsallakawa Amurka.
Rahotanni sun bayyana cewa ayarin mutanen 24, 6 ne mata tare da kananan yara kuma mutane 20 sun fito ne daga Haiti sai kuma 4 da Guinea.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu