Korea ta Arewa-Amurka

Trump ya aike da wasika zuwa Kim Jong Un

Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un da Donald Trump na Amurka
Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un da Donald Trump na Amurka SAUL LOEB / AFP

Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un a yau lahadi ya bayyana farin cikin sa da kuma gamsuwa bayan da ya karbi wata wasika da sunan Shugaban Amurka Donald Trump.

Talla

Kamfanin dilancin labaren korea ta Arewa ya ruwaito cewa Shugaba Kim ya bayyana farin cikin sa yan lokuta da karanta wasika tareda yabawa hangen nisa da Shugaban Amurka yayi karma dai yada yake rubbuce a wasikar.

Ya zuwa yanzu fadar shugaban Amurka ba ta ce upon ba dangane da sahihancin wanna wasika, sai dai hukumomin Korea ta kudu sun yaba da yada ake ci gaba da samu fahimta tsakanin Amurka da Korea ta Arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI