Amurka- Iran

Pompeo na Amurka na ziyara a kasashen Larabawa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo REUTERS/Fabrizio Bensch

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya isa Saudiya domin tattaunawa da mahukuntan kasar a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun tankiya tsakanin Amurka da Iran.

Talla

Ana sa ran Mr. Pompeo zai gana da Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a birnin Jeddah kafin daga bisani ya zarce Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kasashen Saudiya da Daular Laabawa na goyon bayan Amurka wajen daukan matakai masu tsauri akan Iran wadda a makon jiya ta kakkabo jirgin Amurka mara matuki, abinda ya sa shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin kaddamar da harin soji kan Iran.

Kodayake daga baya, shugaban ya dakatar da sojojin daga kai harin bayan ya sauya matsayinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.