Amurka

Amurka ta sake sanyawa Iran takunkumi bayan kakkabo mata jirgi

Donald Trump na Amurka banya sanya hannu kan dokar da ta sahale sake kakabawa Iran takunkumai
Donald Trump na Amurka banya sanya hannu kan dokar da ta sahale sake kakabawa Iran takunkumai REUTERS/Carlos Barria

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da sabbin takunkuman karya tattalin arziki kan Iran a yammacin jiya Litinin, a wani mataki na mayar da martini kan kakkabo jirgin Amurkan da Iran ta yi cikin makon jiya.

Talla

Sabbin takunkuman wadanda ke matsayin martini kan kakkabo jirgin Amurka marar matuki da Iran ta yi, a wannan karon sun shafi hatta jagoran juyin-juya halin kasar ta Iran Ayatollahi Ali Khamne’I, baya ga wasu manyan jami’an kasar ta Iran.

Cikin yammacin jiya Litinin ne, shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan wata dokar gaggawa da ta amince da kakabawa Iran sabbin takunkuman wadda a karon farko ta shafi jiga-jigan mutane a kasar.

Alaka dai ta kara tabarbarewa tsakanin kasashen biyu ne, tun bayan da Iran ta kakkabo jirgin Amurka marar matuki wanda ta zarga da yi mata leken asiri bayan shiga sararin samaniyarta, wanda kuma tun a lokacin Donald Trump ya ce tabbas Tehran ta yi gagarumin kuskure.

Kafin wannan mataki na takunkumi dai sai da Amurkan ta yi kutse a na’urorin da Iran ta yi amfani da su wajen kakkabo jirgin tare da lalata su.

Kasashen duniya da dama dai na ci gaba da suka kan sabon takunkumin na Amurka, ciki kuwa har da Rasha wadda ta bayyana takunkumin da wanda ya sabawa dokokin duniya.

Karkashin sabbin takunkuman, Amurka ta haramtawa kowacce kasa sayen man Iran baya da daura damarar kwace wasu manyan kadarorin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.