Amurka na fatan kulla yarjejeniya da Kungiyar Taliban
Wallafawa ranar:
Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya bayyana fatar kulla yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar Taliban a Afghanistan kafin ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa.
Mike Pompeo da ya samu ganawa da shugaba Ashraf Ghani da Janar Scott Miller dake jagorancin sojin Rundunar Nato a ziyarar bazata da ya kai Kabul, Pompeo ya bayyana cewar zaman lafiya shine abinda Amurka ta sanya a gaba.
A watan Afrilun shekarar bana ,wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar , a cikin watanni uku na farkon wannan shekarar ta 2019, dakarun kawancen da ke goyon bayan gwamnatin Afghanistan sun kashe fararen hula 305, yayinda kungiyoyin ‘yan ta’adda suka kashe mutane 227.
An hallaka akasarin fararen hular ne ta hanyar kaddamar da farmakin jiragen sama ko kuma ta hanyar samamen kasa da dakarun da ke samun goyon bayan Amurka suka gudanar, kuma masu aikata wannan laifin na kauce wa fuskantar hukunci kamar yadda Majalisar ta Dinkin Duniya ta ce.
Ana saran komawa teburin tattaunawa tsakanin wakilan Amurka da Taliban ranar 29 ga watan nan a Doha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu