An murkushe yunkurin juyin mulki a Venezuela
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Venezuela ta sanar da cewar ta murkushe wani yunkurin juyin mulki, inda take zargin kasashen Amurka da Colombia da kuma Chile da hannu wajen kitsa shi domin kashe shugaban kasa Nicolas Maduro.
Ministan sadarwar kasar Jorge Rodriguez ya ce masu yunkurin juyin mulkin sun hada da kunshi jami’an soji da kuma wadanda suka yi ritaya, kuma an shirya kai shi ne tsakanin ranakun Lahadi da Litinin.
Ministan ya zargi shugaban Colombia Ivan Duque da shirya juyin mulki da kuma yunkurin kashe shugaban kasa, tare da shugaban Chile Sebastine Pinera da kuma mai baiwa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro, John Bolton.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu