Duniya

Mexico ba ta da hurumin hana baki shiga Amurka- Lopez

Wasu daga cikin bakin haure yan kasar Mexico
Wasu daga cikin bakin haure yan kasar Mexico REUTERS/Jose Torres

Shugaban kasar Mexico Andres Manuel Lopez Obrador ya bayyana cewar dakarun kasar 15,000 da za’a jibge a kan iyakar Amurka basu da hurumin hana baki tsallakawa, yayin da ya sha alwashin gudanar da bincike kan zargin tsare mutane da akayi a iyakar kasar a makon jiya.

Talla

Lopez ya shaidawa manema labarai cewar, babu wanda ya bada umurnin tsare mutane, kuma zasu gudanar da bincike kan zargin, saboda ganin hakan bai sake aukuwa ba.

Wannan matsayi dai yayi karo da na ministan tsaron kasar Luis Sandoval wanda ya bayyana cewar tsallaka iyaka ba tare da izini b aba wani laifi bane, amma sukan tsare mutane lokacin bincike kafin mika su ga hukumomin shigi da fice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.