Isa ga babban shafi

Wani mai cin zarafin yara zai sha daurin shekaru 16

Kotu da daure wani dan kasar Norway takewa matasa baraza ta kafar intanet wajen samun hotunan bidiyon batsa
Kotu da daure wani dan kasar Norway takewa matasa baraza ta kafar intanet wajen samun hotunan bidiyon batsa AFP
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris | Ahmed Abba
1 min

Wata kotu a kasar Norway ta daure wani mutum shekaru 16 saboda samun sa da laifin cin zarafin daruruwan yara cikin su harda fyade wanda shine mafi muni da aka taba gani a kasar.

Talla

Kotun ta gano cewar sau tari mutumin mai shekaru 27 kan badda kama ya zama karamar yarinya da kuma kiran kan sa Sandra wajen karbar hotunan bidiyon batsa daga yara maza 460, akasarin su masu shekaru kasa da 16.

Wanda ake zargin wanda alkalin wasa ne, ya amsa wasu daga cikin tuhume tuhumen da ake masa daga cikin zargin da ya shafi yara 270, inda kotun ta daure shi shekaru 16 da kuma bashi umurnin biyan diyyar sama da Dala miliyan 2 ga wasu daga cikin wadanda yaci zarafin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.