Iran-Birtaniya

Iran ta bukaci bayani daga Birtaniya kan kame mata jirgin ruwa

Jirgin ruwan Iran da ake zargi da fasakaurin danyen man fetur zuwa kasar Syria.
Jirgin ruwan Iran da ake zargi da fasakaurin danyen man fetur zuwa kasar Syria. AFP

Cikin bacin rai, Iran ta bukaci jakadan Birtaniya, da ya yi mata bayani, kan dalilan kame jirgin ruwan dakon manta da kasarsa ta yi, a mashigin ruwan yankin Gibraltar.

Talla

Da safiyar ranar Alhamis, hadin gwiwar jami’an yan sanda da na Kwastam a yankin Gibraltar da ke karkashin Birtaniya, suka kame jirgin ruwan kasar ta Iran mai tsawon mita 330, bisa zargin cewa, yana kan hanyar kaiwa Syria danyen mai, abinda ya sabawa takunkuman da kungiyar tarayyar Turai EU ta kakabawa gwamnatin Bashar Al Assad.

Tun a karshen shekarar 2011, kungiyar EU ta kakabawa gwamnatin Syria takunkumai, bayan barkewar yakin basasar, wadanda har yanzu suke aiki.

Ministan harkokin wajen Spain da ke makwabtaka da yankin na Gibraltar, Josep Borrell, ya shaidawa manema labarai cewa, an kame jirgin dakon man na Iran ne bisa umarnin kasar Amurka.

Wannan sabuwar dambarwa ta kunno kai ne, a daidai lokacin da kasashen Turai ke lallabar Iran domin ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar da ke tsakaninsu, da a baya bayan ke barazanar rushewa duk dai saboda tsamin dangatakarta da Amurka da ke dada karuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.