Iran-Birtaniya

Iran ta yi barazanar kama jirgin Birtaniya

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif.
Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif. REUTERS/Khalid Al-Mousily

Yau Juma’a, Iran ta bukaci Birtaniya ta gaggauta sakin jirgin dakon manta da ta kama a mashigin ruwan Gibraltar.

Talla

Bayaga zargin Birtaniya da zama yar amshin shatan Amurka, Iran ta yi gargadin za ta maida raddi mai kaushi, idan Birtaniyar ta ki sakar mata jirgin.

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta shaidawa jakadan Birtaniya Rob Macaire cewa baza ta lamunci rainin kame mata jirgin ruwan da kasarsa ta yi ba, bisa umarnin Amurka, kamar yadda Ministan harkokin wajen Spain Josep Borrell, ya bayyana.

Iran ta kuma yi gargadin cewa muddin Birtaniya ta ki sakin jirgin nata, ba shakka za ta maida raddin kama jirgin ruwan kasar ta Birtaniya, a kowane lokaci.

Da safiyar ranar Alhamis, hadin gwiwar jami’an yan sanda da na Kwastam a yankin Gibraltar da ke karkashin Birtaniya, suka kame jirgin ruwan kasar ta Iran mai tsawon mita 330, bisa zargin cewa, yana kan hanyar kaiwa Syria danyen mai, abinda ya sabawa takunkuman da kungiyar tarayyar Turai EU ta kakabawa gwamnatin Bashar Al Assad.

Sabuwar dambarwa ta kunno kai ne, a daidai lokacin da kasashen Turai ke cikin fargabar barzanar da Iran ta yi na bijirewa yarjejeniyar nukiliyar da suka kulla a 2015, da a yanzu haka ke barazanar rushewa tun bayan ficewar da Amurka ta yi daga cikinta, tare da kakaba mata sabbin takunkuman karya tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.