Iran-Turai

Iran ta yi barazanar sake ketare iyakar tace makamashin Uranium

Wasu ma'aikatan cibiyar sarrafa makamshin Uranium ta Bushehr dake kudancin birnin Tehran.
Wasu ma'aikatan cibiyar sarrafa makamshin Uranium ta Bushehr dake kudancin birnin Tehran. REUTERS/Mehr News Agency/Majid Asgaripour

Hukumar da ke sa ido kan yaduwar makaman nulkiya ta duniya IAEA, tace za ta gudanar da taro kan Iran a mako mai kamawa, bayan da kasar ta ketare daya daga cikin iyakar tace makamashin Uranium, da ke karkashin yarjejeniyar nukilyar data cimma da kasashen duniya a 2015.

Talla

Matakin na IAEA ya biyu bayan bukatar da Amurka ta gabatar na bincikar Iran kan bijirewa yarjejeniyar.

Iran a nata bangaren ta yi barazanar cewa a gobe lahadi zata sake ketare iyakar tace makamashin na Uranium muddin ba’a gaggauta sassauta takunkuman karya tattalin arzikin da Amurka ta kakaba mata ba.

A farkon watan Yuli Hukumar Yaki da Yaduwar Makamin Nukiliya ta IAEA ta tabbatar cewar kasar Iran ta zarce adadin da aka gindaya mata na tace sinadarin Uranium a karkashin yarjejeniyar nukiliyar da kasashen duniya suka kulla da ita a shekarar 2015.

Mai magana da yawun hukumar ta IAEA ya ce, binciken da hukumar ta gudanar, ya nuna cewar Iran ta zarce kilogram 300 na sinadarin wanda ya saba ka’ida.

Shi ma Ministan Harkokin Wajen Iran Javad Zarif ya tabbatar da zarce adadi tace makamashin na Uranium a daidai lokacin da kasar ke barazanar watsi da yarjejeniyar da ta cimma da manyan kasashen duniya a ranar 7 ga wannan wata na Yuli saboda takunkumin da Amurka ke ci gaba da kakaba mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.