Duniya

Yan Sandan duniya sun kai samame mafi girma kan masu laifi

Wasu daga cikin jami'an rundunar Yan Sanda ta duniya.
Wasu daga cikin jami'an rundunar Yan Sanda ta duniya. AFP/TIZIANA FABI

Wani gagarumin samame da Yan Sandan duniya suka kaddamar a kasashe 33 tare da hukumar da ke yaki da masu amfani da kwayoyin da ke kara kuzari, yayi nasarar kwace miliyoyin magungunan da aka haramta amfani da su, tare da kama mutane 234.

Talla

Rundunar Yan Sandan Turai da ake kira Europol ta ce aikin ya shafi kasashe 23 da ke Turai da kuma 10 a sauran sassan duniya da suka kunshi Albania da Colombia da Iceland da Switzerland da kuma Amurka.

Rundunar ta Europol tace adadin haramtattun magungunan da hadin gwiwar jami’an tsaron suka yi nasarar kwacewa yayin samamen ya kai kusan miliyan 4.

Rundunar ta kuma ce yayin gudanar da aikin, sun yi nasarar tarwatsa kungiyoyin tsageru masu aikata laifuffuka 17 da ke safarar kwayoyin a Turai.

Kasar Italiya ce ta jagoranci samamen mafi girma da rundunar Yan Sandan ta duniya ta kai kan masu laifi a kasashe da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI